in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a bayyana wani gagarumin hasahen ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka a wasu kasashen Afrika ba
2018-03-08 10:34:23 cri
A ranar 6 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya sake nanata muhimmancin hadin kai tsakanin kasarsa da kasashen Afirka.

Tillerson ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya yi kafin ziyarar sa a kasashen Afirka karo na farko a cikin wa'adin aikinsa.

Manazarta sun nuna cewa, Tillerson ya kai wannan ziyara da nufin kawar da sabani a tsakanin Amurka da kasashen Afirka, da kuma karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Amma, da kyar a samu nasara kan ziyarar saboda gwamnatin Trump ba ta mai da hankali sosai kan nahiyar Afirka ba, kana ta nuna tsattsauran ra'ayi kan batun bakin haure.

Baya ga haka, manazarta sun nuna cewa, kasashe daban daban na Afirka ba su jin dadi kan Amurka sakamakon tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasashen Afirka da kullum take yi bisa matsayinta na wata babbar kasa, don haka, ba a sa ran wannan matakin da Tillerson ya dauka zai iya yin wani tasiri ko kuma samu nasara ba.

Bisa sanarwar da majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta bayar, an ce, a ranar 6 ga wata, Tillerson ya soma wannan ziyararsa ta kwanaki 8 a kasashe 5, ciki har da Chadi, Djibuti, Habasha, Kenya da kuma Najeriya. Sanarwar ta kuma ce, batutuwan da zai tattauna a yayin ziyarar sun hada da hadin kan yaki da ta'addanci, da inganta zaman lafiya da zaman karko a nahiyar Afirka da kuma ciyar da cinikayya da zuba jari a tsakanin Amurka da Afirka gaba da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China