in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta yiwa kasar Sin binciken hakkin dan Adam zagaye na uku
2018-11-02 18:40:20 cri

Yau Jumma'a, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, daga ranekun 6 zuwa 9 na watan Nuwambar bana, kwamitin kula da hakkokin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, zai gudanar da bincike kan kasar Sin ta fannin hakkokin dan Adam a birnin Geneva.

Lu ya ce, gwamnatin kasar Sin na maida hankali sosai kan binciken na wannan zagaye, kana ta riga ta gabatar da wani rahoto dangane da hakkokin dan Adam na kasar zuwa ga MDD, tare kuma da tura wata tawagar dake kunshe da manyan jami'an gwamnati don halartar binciken, ciki har da mataimakin ministan harkokin wajen kasar, da sauran wakilai daga jihohin Xinjiang, da Tibet, da yankunan Hong Kong da Macao.

Lu ya kara da cewa, kasar Sin za ta nuna himma da kwazo wajen gudanar da shawarwari, tare da bangarori daban-daban a yayin binciken.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China