in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Le Yucheng: Yanayin lura da hakkokin bil Adama na kasar Sin ya samu amincewa daga dukkanin sassa
2018-11-08 11:08:29 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya ce salon martaba hakkokin bil Adama na kasar Sin, ya samu karbuwa da fahimta, da amincewa daga sassa daban daban.

Le Yucheng ya ce tawagar wakilan kasa da kasa karkashin MDD, mai lura da hakkin bil Adama, ta nazarci rahoton kula da hakkin bil Adama na kasar Sin a karo na 3 a ranar Talata, bayan gudanar da makamancin sa a shekarun 2009 da 2013.

Yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Le wanda kuma shi ne jagoran tawagar Sin, ya ce cikin kasashe 150 da suka nazarci rahoton, sama da 120 sun nuna goyon bayan su ga matakan da Sin ke dauka.

Ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, yayin da Sin ke aiwatar da sauye sauye, da bude kofa ga kasashen waje, kasar ta aiwatar da matakai na kyautata yanayin lura da hakkokin bil Adama, tana kuma bunkasa dimokaradiyya, da kyautata rayuwar al'umma, tare da bin tafarkin ci gaba bisa halayyar musamman ta Sin.

Game da shakku da wasu kasashen yammacin duniya ke nunawa, bisa halin da ake ciki a yankin Xinjiang, Mr. Le ya ce an kaddamar da cibiyar horaswa ta yankin Xinjiang ne, domin ilimantar da al'umma, ta yadda za su kaucewa rungumar ayyuka masu nasaba da tsattsauran ra'ayin addini.

Kaza lika shirin na taimakawa wajen sauya tunanin wadanda ke da tsattsauran ra'ayin, har su kai ga komawa rayuwa mai inganci. Kaza lika shirin wani mataki ne na kandagarki, kana gudummawa ce ta Sin a aikin yaki da tsattsauran ra'ayi na kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China