in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman dakon kayayyaki maras matuki na farko a duniya ya tashi cikin nasara
2017-11-01 13:10:55 cri

Jirgin saman dakon kayayyaki maras matuki na farko samfurin AT200, ya tashi a birnin Xi'an dake lardin Shaanxi na kasar Sin a ranar 30 ga watan Oktoba. Hakan dai ya alamta cewa, Sin ta cimma nasarar nazarin jirgin saman dakon kayayyaki maras matuki.

An ce, nauyin kayayyakin da irin wannan jirgin saman ka iya dauka ya kai ton 1.5, kuma saurin tafiyarsa ya iya kai kilomiya 313 a kowace sa'a, wanda kuma ka iya yin tafiyar da ta kai tsawon sa'o'i 8 a kowane karo, tafiyar da nisan ta zai kai kilomita 2183.

Yayin da yake dauke da kayayyaki, jirgin na iya tashi ko sauka a cikin tsawon mita 200, don haka an warware matsalar tashi da saukar jiragen saman dakon kayayyaki maras matuka, a yankin duwatsu na yammacin kasar Sin ko tsibiran kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China