in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron yanar gizo na duniya karo na 5
2018-11-09 20:03:55 cri

A yau ne aka rufe taron yanar gizo na duniya karo na 5 a birnin Wuzhen na lardin Zhejiang na kasar Sin

A yayin taron da aka shafe kwanaki uku ana yi, wakilai kimanin 1500 daga kasashe da yankuna 76 suka halarta, inda suka yi musayar ra'ayoyi da tattaunawa gami da cimma daidaito kan batun samar da yanayin yin imani da juna da yadda za su rika sarrafa yanar gizo da kansu da kokarin raya fito da tsarin yanar gizo na bai daya.

Haka kuma a yayin taron an gabatar da rahoton bunkasuwar yanar gizo ta kasar Sin na shekarar 2018 da rahoto a wannan fanni na duniya, wadanda suka maida hankali ga halin da yanar gizo ke ciki a gida da waje, da samar da sabon tunani da goyon baya a fannin fasahohi ga bunkasuwar yanar gizo a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China