Wadannan manyan kamfanoni sun hada da manhajar aikewa da sakonnin sada zumunta Wechat, Weibo mai kama da Twitter, da kamfanonin cinikayya ta yanar gizo na Taobao da Jingdong, kamfanin motocin hayar taksi na Didi da taswirar nan ta Baidu.
A jiya ne hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta majalisar zartaswar kasar Sin, da ma'aikatar kula da masana'antu da bayanan kimiya, ma'aikatar tsaron jama'a da ingancin kayayyaki suka sanar da sabon sakamakon game da manufofin tsaron wadannan kamfanoni.
A karshen watan Yuli ne hukumomi suka kaddamar da bincike kan ayyukan kamfanonin, ta yadda za su kara inganta manufofinsu na tsaro. Mahukuntan kasar Sin na fatan kamfanonin za su ci gaba da inganta manufofinsu na tsaro, yayin da a hannu guda gwamnati za ta rika gudanar da bincike a kai a kai don tabbatar da cewa, suna tafiyar da harkokinsu kamar yadda doka ta tanada. (Ibrahim Yaya)