in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Zambia: Bikin baje kolin shigo da kayayyaki kasar Sin ya bude kofa ga kasuwannin duniya
2018-11-06 10:38:13 cri
Bikin baje kolin kasa da kasa na shigo da kayayyaki kasar Sin wato (CIIE), wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Shanghai, wata babbar dama ce wajen kara bunkasa cigaban kasa da kasa, in ji wani kwararre kan tattalin arziki a kasar Zambia.

Masanin ya bayyana farin cikinsa bisa yadda kasar Sin ke cigaba da bude kofarta domin shigo da hajoji daga kasashen ketare.

Lubinda Haabazoka, wanda shine shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasar Zambia (EAZ) ya ce, "Wannan wani sabon abu ne kuma muna maraba dashi. Hakika zai baiwa sauran kasashen duniya damar su ma su bude kasuwanninsu ".

Haabazoka ya nanata cewa, bikin baje kolin shigo da kayayyakin ya nuna yadda kasar Sin ta bude kofarta, wanda wannan shine babban ruhin kungiyar cinikayya ta kasa da kasa WTO.

Fumba-Makano, malama ce a cibiyar Dag Hammarskjold ta nazarin wanzar da zaman lafiya da magance rikice rikice a jami'ar Copperbelt ta kasar Zambia. Ta yabawa gwamnatin kasar Sin saboda bude kofarta ga duniya, tana mai cewa "wasu bangarorin duniya suna ba da kariya ga cinikayya, amma ita kasar Sin tana bude kofarta ga kasa da kasa".

Kwararrun sun kara jaddada cewa, baje kolin zai kara taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin duniya sakamakon yadda yake karfafa gwiwa ga sauran sassan duniya wajen yin watsi da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, wanda hakan ba zai haifar da da-mai-ido ba ga cigaban tattalin arzikin duniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China