Wannan bikin baje kolin na CIIE da shugaba Xi Jinping ya ba da shawarar shiryawa ya kuma kaddamar da shi a yau, ya kasance wani babban bikin baje koli na kasa dake dora muhimmanci kan shigo da kayyayaki na farko a duniya, burinsa shi ne samarwa kasashe daban daban wani dandamali wajen amfani da damar ci gaban kasar Sin, da zurfafa hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa, da kuma tabbatar da samun wadata tare, shi ne kuma wani hakikanin aiki da Sin ta dauka wajen bude kofa a fannin tattalin arzikin duniya, da goyon baya kan dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. (Bilkisu)