Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yau Litinin a birnin Shanghai, cewar bikin CIIE bikin baje koli ne irin sa na farko a duniya, wanda aka mayar da batun shigowa da kayayyaki a matsayin babban takensa, don haka ya kasance wani babban ci gaba a tarihin cinikayyar kasa da kasa.
Xi yana ganin cewa, shirya bikin CIIE wata babbar manufa ce da kasar Sin ta fitar, wajen bude kofa ga waje, kuma wani muhimmin mataki ne da Sin ke dauka, wajen bude kasuwarta ga duniya. Lamarin da ya shaida matsayin kasar Sin, na goyon bayan tsarin yin cinikayyar kasa da kasa, da sa kaimi ga yin ciniki maras shinge. (Kande Gao)