Rahoton wanda aka fitar ranar 31 ga watan Oktoba, ya kuma bayyana cewa, yawan kwaskwarimar da kasar Sin ta yi don kyautata yanayin kasuwanci na matsakaita da kanana kamfanoni a cikin shekara daya da ta gabata, ya sa kasar ta kasance matsayi 10 dake gaba a duniya a wannan fannin.
Rahoton ya shaida cewa, kasar Sin ta fi samun kyautatuwa a fannonin kafa kamfanoni da samar da wutar lantarki a cikin manyan fannoni 10 da aka yin bincike kansu. Matsayin Sin a fannin kafa kamfanoni ya daga daga 93 zuwa 28, kuma matsayinta a fannin samar da wutar lantarki ya daga, daga 98 zuwa 14. Hakazalika, kasar Sin ta yi kwaskwarima mai amfani a fannonin bayar da iznin yin gine-gine, yin rajistar dukiya, da bada tabbaci ga wasu masu zuba jari, da buga haraji, da kuma ciniki a tsakanin kasa da kasa.
Rahoton yanayin kasuwanci, muhimmin rahoto ne na bankin duniya, da a kan gabatar a kowace shekara. Daga shekarar 2003, zuwa yanzu, an gabatar da rahotanni 16. (Zainab)