in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu bukatar Sin ta sarrafa farashin musayar kudin RMB
2018-07-31 10:58:02 cri
Dangane da zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin cewa, tana sarrafa farashin musayar kudin RMB, a kwanakin baya, babban masanin tattalin arzikin Asusun ba da lamuni na IMF Maurice Obstfeld ya yi bayani cewa, babu shaida ko kadan da ya nuna cewa, Sin tana sarrafa farashin musayar kudinta.

A hakika dai, zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin ba shi da tushe, kana ya saba da gyare-gyaren da kasar Sin ta yi kan tsarin farashin musayar kudin RMB. Kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, farashin musayar kudin Sin na canjawa ne bisa yanayin kasuwanni, kuma, Sin ba ta son fitar da karin hajoji zuwa ketare ta hanyar rage farashin musayar kudin RMB. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China