Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake gabatar da umarni, game da bunkasa ginin yankunan ciniki maras shinge na kasar ta Sin.
Ya ce bunkasar wadannan yankunan ciniki, daya ne daga muhimman matakan da kwamitin koli na JKS ke dauka, wajen fadada gyaran fuska, da kara bude kofa ka kasashen waje a sabon zamani da ake ciki, ya kuma zama wani jigo na cimma nasarar hakan.
Shugaban ya kara da cewa, bayan shekaru 5 da aiki tukuru, a fannin bunkasa yankunan cinikayya cikin 'yanci na Sin, an kai ga cimma manyan nasarori, wadanda suka baiwa kasar damar tunkarar matakan inganta harkokin gudanarwa.
Daga nan sai shugaban na Sin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a fannin, da su dauki karin matakan hanzarta ci gaban yankunan cinikayya cikin 'yanci, ta yadda hakan zai inganta kirkire kirkire, wadanda za su kai ga cimma manyan burikan kasar guda biyu na shekaru 100, da kuma na sake farfado da kasar baki daya.