in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddamar ciniki ta kawo babbar illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2018-09-17 10:30:25 cri
A yayin taron tattaunawa kan bunkasuwar kasar Sin na shekarar 2018 da aka bude jiya Lahadi, masanan tattalin arzikin Sin da dama suna ganin cewa, takaddamar ciniki ta kawo illa ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban na duniya a halin yanzu, kuma za ta iya haifar da rikicin hada-hadar kudi, har ma da illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da ake kokarin farfadowa.

Mataimakin direktan cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa ta majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yiming ya bayyana a gun taron tattaunawar cewa, bisa rahoton hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya da bankin duniya ya gabatar a ranar 5 ga watan Yuni na shekarar 2018, harajin kwastam ya karu a yawancin sassan duniya, wanda ya kawo babbar illa ga harkokin cinikayya a duniya, abin da zai sa ya zuwa shekarar 2020, yawan harkokin cinikayya a duniya ya iya raguwa da kashi 9 cikin dari.

Wang Yiming na ganin cewa, karuwar takaddamar ciniki, zai yi babban tasiri kan sauran hadarru a duniya, kuma hakan zai kara haifar da rashin tabbas ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Tsohon mataimakin shugaban kwalejin kimiyyar zamantakewar al'umma na kasar Sin kuma masanan tattalin arzikin kasar Li Yang yana ganin cewa, rikicin cinikin da kasashe da dama suke fuskanta zai tsananta hadarin basussuka na tattalin arzikin duniya, kana zai rage karfin bunkasuwar tattalin arziki da kawo babbar illa ga wannan fanni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China