in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe mambobin WTO sun nuna damuwa game da karin haraji da Amurka ta sanya kan wasu hajoji
2018-04-24 10:32:42 cri
Kasashe mambobin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, sun nuna damuwa game da matakin Amurka, na kara haraji kan hajojin karafa da na gangar ruwa.

Kasashen da suka hada da Sin da Rasha, da India, da Venezuela, da Turkey, da Norway, da Switzerland, da Singapore, sun bayyana rashin gamsuwa da matakin na Amurka ne, yayin taron kwamitin samar da kariya ga mambobin kungiyar ta WTO da ya gudana a jiya Litinin.

Kasar Sin ce dai ta fara gabatar da kashedi, game da tasirin kuduri mai lamba ta 232, wanda Amurka ta yi amfani da shi wajen kara harajin, tana mai cewa hakan zai haifar da gagarumar matsala ga tsarin cinikayyar kasa da kasa, zai kuma katse musayar hajojin da kasashen duniya ke gudanarwa bisa doka.

A nata bangare, Rasha ta ce tsarin da aka bi na sanya harajin mai dace ba, zai kuma yiwa hajojin kasashen waje tarnaki, kana ba a baiwa kamfanonin dake samar da irin wadannan hajoji damar fadin albarkacin bakin su ba.

Ita kuwa Turkiya cewa ta yi, kamata yayi kasashe mambobin kungiyar G20 dake hada hadar cinikayyar karafa, su samar da wata kafa ta tattauna wannan matsala, tana mai cewa, shawarwari ne kadai za su warware wannan takaddama maimakon daukar matakai na kashin kai.

To sai dai kuma a nata bangare, Amurka ta ce harajin da ta sanyawa wadannan hajoji, na da nasaba da matakan tsaron kasa, amma ba wai na kandagarki ba ne. Don haka babu bukatar gudanar da wasu shawarwari tsakanin ta da sauran mambobin kungiyar ta WTO, karkashin manufar samar da kariyar cinikayya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China