in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gidan Talabijin na kasar Mozambique zai fara yada labarai cikin harsunan gargajiya
2018-10-30 12:37:53 cri
Gidan talabijin na kasar Mozambique TVM, ya sanar da cewa daga yanzu, zai fara yada labarai cikin harsuna 15 a fadin kasar.

A cewar Jami'in dake kula da shirye-shirye na gidan TVM Claudio Jone, da farko, gidan talabijin din zai yada labarai daga ranekun Litinin zuwa Juma'a, inda a kullum za a yada labarai cikin harsuna 3, inda a karshen mako, za a samu adadin harsuna 15.

Yada labarai bisa amfani da harsunan kasar a gidan TVM na da nufin biyan bukatun masu kallo, wadanda aka kawo wani lokaci da ba sa samun labarai cikin harsunansu na uwa.

Jami'in ya ce fara gabatar da labarai cikin harsunan gargajiya zai kara ba 'yan kasar damar shiga harkokin siyasa.

Duk da cewa kasace dake amfani da harshen Portuguese, ya ce shirin na yada labarai cikin harsunan gargajiya ya hada da ne da kara tafiya da zamani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China