A jawabin da ya gabatar, shugaba Filipe Nyusi, ya bayyana ginin titin a matsayin cikar buri na bai daya na tsoffin shugabanni da jama'ar kasashen biyu.
Bankin raya nahiyar Afrika ne ya samar da kudin ginin titin da ya kunshi ginin gadoji uku, da za su saukaka zirga-zirgar mutane da hajoji, tare kuma da bada gudummawa ga harkar yawon bude ido, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arzikin yankin.
Shugaban ya kara da cewa, titin zai bunkasa cinikayya a kasar, da ma wadda ake yi tsakaninta da makwabciyarta Tanzania, tare kuma da taimakawa wajen rage fatara.
Rukunin kamfanin gine-gine na Anhui Foreign Economic Construction na kasar Sin ne zai gudanar da aikin, inda kuma zai dauki yawancin ma'aikatansa a yankin. Shugaban ya bukaci wadanda za a dauka aikin su kasance masu kwazo. (Fa'iza Mustapha)