in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Mozambique sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da darajarta ta kai dala miliyan 100
2018-06-05 09:26:57 cri
Gwamnatin kasar Sin da ta Mozambique, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar gudanar da ayyuka 4, da za su lakume dala miliyan 100 a Mozambique.

An cimma yarjejeniyar ce a jiya Litinin, yayin wani taron hadaddiyar kwamitin kula da tattalin arziki da fasahohi da huldar cinikayya na kasashen 2.

Mataimakin ministan ciniki na kasar Sin, Qian Keming, da mataimakiyar ministan harkokin wajen Mozambique, Maria Lucas ne suka jagoranci taron.

Yarjejeniyar ta shafi ayyuka 4 da suka hada da gina wata kwalejin fasaha a tsakiyar lardin Sofala da filin jirgin sama na Xai-Xai da hadin kai ta fuskar samar da kayayyakin fasaha a filin wasannin na kasar da kuma hadin kai da tuntubar juna tsakanin kwararru a fanni noma.

Kasashen Sin da Mozambique sun cimma yarjejeniya kan kare hannayen jari, inda a shekarar 2001, suka fara aiwatar da tsarin kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki da cinikayya. A yanzu, kasar Sin ita ce ta farko wajen yawan jari da aka zuba a Mozambique, kuma ita ce babbar abokiyar huldarta ta kasuwanci, kana daya daga cikin muhimman masu samar da kudin gudanar da ayyuka da kuma aikin ginin kayayyakin more rayuwa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China