in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar al'adun Sin dake Mozambique za ta zama sabuwar alamar Maputo
2018-05-14 09:33:11 cri

Cibiyar al'adun kasar Sin dake Maputo, hedkwatar kasar Mozambique ta kasance gini mafi girma da Sin take ba da taimako wajen gina shi a Mozambique a halin yanzu. Fadin filin wannan gini ya kai muraba'in mita dubu 20, ban da cibiyar al'adu, akwai kuma dandalin shirya wasan kwakwayo dake iya daukar 'yan kallo 1500, da dakin karatu da dai sauran dakuna a fannoni daban-daban.

An gina cibiyar ce bisa al'adun Sin da Mozambique baki daya, wato gini ya yi kama da wani mafifici na kasar Sin, haka kuma mutane za su yi amfani da filin dake gaban gini wajen gudanar da taro, dukkanin ginshigai masu launin rawaye na ginin, an tsara su ne bisa salo irin na Afrika. Hakazalika, launin ja da aka yi amfani da shi da tagogin ginin salo ne na kasar Sin dake bayyana tarihin gini iri na Sin.

Cibiyar za ta kasance jerin gine-gine ne dake kunshe da ayyukan wasannin kwaikwayo da mu'ammalar al'adu baki daya, bayan an kammala wannan gini, zai zama wani dandali na musamman ne wajen yin musanyar al'adu tsakanin kasashen biyu da nune-nunen al'adun Sin masu tarihi. Haka kuma zai zama wata sabuwar shaidar sada zumuncin gargajiya tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China