Shugaban cibiyar nazarin tsaron jama'a ta Mozambique(INSS) kana jagoran macin, Francinsco Mazoio ya shaidawa kamfanbin dillancin labarai na Xinhua cewa, bikin ya kayatar, duk da bukatun da ma'aikata suka gabatar game da albashi da inganta yanayin aiki.
Ya ce, har yanzu akwai jan aiki game da abin da ya shafi ma'aikata, inda ya ba da misali da yadda ake ci gaba korar ma'aikata ba da wani kwakkwaran dalili ba.
Shi ma a nasa jawabin babban sakataren kungiyar kwadago ta kasar Mozambique, Alexandre Munguambe, ya ce babban kalubalen da kungiyar take fuskanta, shi ne yadda za ta sasanta da gwamnati game da karin mafi karancin albashin, a daidai lokacin da gwamnati ke fama da matsalar tattalin arziki. (Ibrahim)