in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana na sa ran ganin bikin Expo da zai gudana a Shanghai zai taimakawa aikin ciniki
2018-10-29 10:53:49 cri
Hukuma mai kula da neman jari da raya aikin ciniki ta kasar Botswana tana sa ran ganin yadda kasar ta halarci bikin Expo na nuna kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen waje zai taimakawa raya huldar ciniki dake tsakaninta da kasar ta Sin. Kutlo Moagi, ita ce mai magana da yawun cibiyar karfafa zuba jari da cinikayya ta kasar Botswana BITC, wadda ta gaya ma wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bikin Expo din da zai gudana tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba mai zuwa, a birnin Shanghai na kasar Sin, zai samar da damammaki na ciniki da raya tattalin arziki ga kasar Botswana. Jami'ar ta kara da cewa, kasar Sin ita ma ta nuna aniyarta ta zama babbar abokiyar ciniki mafi muhimmanci ta kasar Botswana nan gaba kadan. A cewar madam Moagi, cibiyar BITC na neman kulla hulda tsakanin kamfanoni masu sarrafa kayayyaki na kasar Botswana da takwaransu na kasar Sin, ta yadda a nan gaba za a samu damar samar da karin kayayyaki a masana'antun dake Botswana. An ce a wajen bikin Expo din da zai gudana a Shanghai, za a samu halartar kamfanoni fiye da 2800 na kasashe da yankuna 130, gami da masu sayen kaya 160,000, da suke wakiltar kamfanoni fiye da 80,000 na cikin gida da na kasashen waje. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China