Sanya hannu kan yarjejeniyar ya kasance a matsayin cigaban da aka samu a kokarin da aka fara bisa ga bukatar da aka mikawa hukumar gudanarwar AU a shekarar 2015, kamar yadda AU din ta sanar a ranar Laraba.
Kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ta yabawa yarjejeniyar da cewa kyakkyawan yunkuri ne, kuma abin koyi ne ga dukkan mambobin kasashen kungiyar wajen warware dukkan takaddama da ta shafi kan iyakokin kasashen.
Sanarwar ta ce, sanya hannu kan yarjejeniyar ba kawai za ta kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen Botswana da Namibia ba ne, har ma za ta kara aniyar kasashen biyu na kyautata yanayin mu'amala tsakanin alummominsu da kuma samar da cigaba ga kasashen masu makwabtaka da juna.