in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar malaria ta barke a yankunan tsakiya da kudancin Botswana
2018-04-23 10:50:44 cri
Ma'aikatar lafiyar kasar Botswana, ta ce an samu barkewar cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria a yankunan tsakiya da kudancin kasar.

Da yake zantawa ta wayar tarho da kamfanin dallancin labarai na Xinhua, babban jami'in ma'aikatar Tjantilli Mosweunyane ya ce a cikin makon da ya gabata, an samu akalla mutane 35 da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda ya ce jami'an lafiya na daukar matakan dakile ta'azzarar cutar.

Ya kara da cewa, an gargadi al'ummar kasar game da barkewar cutar, musammam a yankunan tsakiya da kudanci inda ta fi kamari, saboda mamakon ruwan sama da aka samu.

Duk da cewa kawo yanzu babu wanda ya mutu sanadin cutar, Jami'in ya ce cutar Maria cuta ce mai tsanani da ake samu daga cizon sauro, wanda kuma kan haddasa asarar rai idan aka gaza shan magani da wuri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China