A cewar shugaban, kasar Sin ta dauki manyan tsare-tsaren rage talauci, wadanda suka taimaka wajen inganta rayuwar mutane da yawa. Bisa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi, an yi nasarar fitar da dimbin jama'ar kasar Sin daga kangin talauci, wanda ya kasance wani babban ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba a duniya.
Kafin ya zama shugaban kasa, mista Masisi ya taba kula da aikin rage talauci. A cewarsa, kasar Botswana ta koyi fasahar kasar Sin ne don tsara shirin rage talauci a gida. (Bello Wang)