Da yake ganawa da makiyaya a Francistown, birni mafi girma na 2 a kasar, Ministan ya ce gwamnati na duba yuwuwar fadada kasuwarta na fitar da naman sa.
Botswana kan samar da akalla ton 24,000 na naman sa a kowacce shekara ta hannu kamfaninta dake sarrafa nama, inda take sayarwa da shi a ciki da wajen kasar.
Kimanin ton 9,000 na naman ake fitarwa nahiyar Turai, kuma kasar a yanzu, na son sayar da naman a karin kasuwanni dake yankinta da ma duniya baki daya.
A don haka ne Ministan ya ce kasar ta dauki wani lokaci ta na bibiyar kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)