in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF zai kara matakan yaki da Ebola a DR Congo
2018-09-14 20:36:33 cri

Asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) ya sanar a yau Jumma'a cewa, zai bude wani sabon sashen tunkarar cutar Ebola a Jamhuriyar demokiradiyar Congo, domin taimakawa dubban mutane, ciki har da kananan yara, sakamakon rahoton baya-bayan dake nuna cewa, an sake samun bullar cutar a kasar.

A wani labarin kuma, mahukuntan Congo sun sanar a jiya Alhamis cewa, an kara samun rahotannin bullar cutar guda biyar, ciki har da biyu daga birnin kasuwanci na Butembo dake lardin arewacin Kivu, guda daga ciki ma'aikacin lafiya ne dake aiki a wani karamin asibiti inda aka fara magance cutar ta farko a birnin.

Asusun na UNICEF ya bayyana cewa, fadada matakan yaki da cutar gami da tura tawagar kwararru mai mutum 11 a fannin ilimantar da al'umma da kwantar da hankunan jama'a da samar da ruwa da tsaftar muhalli da kiwon lafiya don taimakawa wajen dakile cutar da ma hana yaduwarta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China