Kwararru a fannin kiwon lafiya na yankin gabashin Afirka karkashin hukumar lafiya ta duniya WHO, sun fara wata ganawa ta musamman a jiya Talata a kasar Uganda, domin musayar bayanai game da sake barkewar cutar Ebola mai saurin kisa, a Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Ofishin WHO dake Uganda ya fitar da wata sanarwa game da hakan, yana mai cewa kwararru daga kasashen Uganda, da Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Sudan ta kudu da Somalia, sun fara nazari game da ayyukan sa ido, don gane da cututtukan Ebola da shan Inna ko Polio.
Wani rahoto da aka fitar a ranar 23 ga watan Satumbar nan, ya nuna cewa cutar Ebola ta hallaka mutane a kalla 69, baya ga wasu 31 da ake zaton cutar ce ta hallaka su, tun bayan da ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar dimokaradiyyar Congon ta ayyana sake barkewar ta a lardin arewacin Kivu cikin makon jiya.
Ebola cuta ce da wasu kwayoyin virus ke haddasawa, wadda kan haifar da zazzabi, da amai da gudawa, da kuma zubar jini ta kafofin jikin wanda ya kamu da ita.(Saminu Alhassan)