An ayyana barkewar cutar a arewacin lardin Kivu ne a ranar 1 ga watan nan, kuma UNICEF ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu, yara 2 sun mutu, yayin da wasu 6 wadanda ake zargin sun kamu da cutar ke karbar magani a wasu cibiyo biyu dake yankin.
Asusun UNICEF da abokan huldarsa, sun horar da jami'ai 90 da suka kware kan nazarin tunani da za su taimaka wajen kula da yara a cibiyoyin kula da masu cutar Ebola.
Wadannan kwararru za kuma su taimakawa yaran bayan an sallame su, wadanda ka iya fuskantar tsangwama a cikin al'ummominsu. Sun kuma shirya gangamin wayar da kai domin saukaka komawar yaran.
Baki daya dai, mutane 70 aka tabbatar ko kuma ake zargin sun kamu da Ebola a yankin arewacin Kivu, inda 44 suka mutu. Har ila yau, akwai wasu 24 da ake jiran sakamakon gwajin da aka yi musu. (Fa'iza Mustapha)