in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shehun malami na kasar Najeriya na son koyon fasahar rage talauci ta kasar Sin
2018-10-25 11:22:46 cri

Duk a wajen taron dandali na Wanshou dake gudana a birnin Beijing na kasar Sin, Dokta Efem Nkam Ubi, darektan sashen huldar kasa da kasa a fannin tattalin arziki na cibiyar nazarin al'amuran duniya ta kasar Najeriya, ya fada a jiya Laraba cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin rage talauci, ta yadda za su samu damar tabbatar da ci gaban kansu.

Shi dai Dokta Ubi, ya taba karatu a kasar Sin har tsawon shekaru 3. A cewarsa, duk lokacin da ya zo kasar Sin ya kan ga wasu sauye-sauyen da aka samu a fannoni daban daban. Ban da haka, ya ce yana mamaki kan ci gaban da kasar Sin ta samu bayan ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje wasu shekaru 40 da suka wuce, gami da yadda kasar ta samu fitar da mutane miliyan 600 daga kangin talauci cikin shekaru 30 da suka wuce. A ganinsa dalilin da ya sa kasar ta samu wannan ci gaba, shi ne domin shugabannin kasar suna kokarin cika alkawuran da suka dauka, gami da daukar takamaiman matakai wajen raya kasa.

Dokta Ubi ya kara da cewa, tsakanin kasar Najeriya da kasar Sin akwai abubuwa masu yawa wadanda suka yi kama da juna. Don daidaita yanayin da take ciki, ya kamata Najeriya ta daina dogaro kan albarkatun mai fiye da kima, gami da raya tattalin arzikin kasar na fannoni daban daban, musamman ma aikin gona, da matsakaitu da kananan kamfanoni masu zaman kansu, gami da fannin gina kayayyakin more rayuwar jama'a. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China