in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan kungiyar editocin tarayyar Najeriya na ziyara a kasar Sin
2017-07-26 15:43:51 cri

A halin yanzu, wasu wakilai biyar daga kungiyar editocin tarayyar Najeriya na wata ziyara a nan kasar Sin.

Tawagar dake karkashin jagorancin Madam Funke Egbemode, ta ziyarci wani sansanin raya sana'o'i da suka shafi sabbin hanyoyin watsa labarai a birnin Beijing, inda suka kara fahimtar yadda sana'o'in bunkasa al'adu ke gudana bisa fasahohin zamani a kasar Sin.

Har wa yau, wannan tawaga ta kai ziyara ofishin kamfanin sadarwa na StarTimes dake nan Beijing, inda bangarorin biyu suka kuduri aniyar fadada hadin-gwiwa a fannin watsa shirye-shirye tsakaninsu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China