Cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamitin ya jinjinawa tanade-tanaden yarjejeniyar da aka sanyawa hannu ranar Litini da ta gabata, wadanda suka jaddada kudurin MDD na bada cikakken goyon baya ga aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu a kasar Mali.
Kwamitin ya kuma yi maraba da sabon kudurin gwamnati da na kungiyoyin masu dauke da makamai, na gaggauta aiwatar da yarjejeniyar, inda ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe don inganta samar da zaman lafiya mai dorewa da kare hakkokin bil adma da magance kalubalen tsaro da na ci gaba. (Fa'iza Mustapha)