in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Faransa ya rasu sakamakon wani hadari
2018-10-18 19:39:48 cri
Ma'aikatar tsaron kasar Mali, ta sanar da rasuwar wani sojin kasar Faransa mai suna kofir Abdelatif Rafik, sakamakon hadari da ya rutsa da shi yayin da yake bakin aiki.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce Abdelatif Rafik yana kusa da wata tayar mota ne da ya kammala gyara, sai kawai tayar ta yi bindiga, kuma nan take hakan ya yi sanadiyyar rasuwar sa.

Kasar Faransa ta fara daukar matakan soji ne a kasar Mali tun daga shekarar 2013, domin dakile ayyukan masu tsattsauran ra'ayin Islama, dake tada zaune tsaye musamman a yankunan Arewacin kasar, bayan da suka amshe iko da wani sashe na yankin a shekarar 2012. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China