in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya nuna damuwa game da barkewar rikici a tsakiyar Mali
2018-06-27 11:11:44 cri
Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric yace sakatare janar na MDDr Antonio Guterres ya bayyana damuwa game da barkewar rikicin kabilanci a tsakanin al'umma da kuma take hakkin dan adam a tsakiyar kasar Mali.

Kakakin yace babban sakataren ya nuna damuwarsa ne bayan da aka samu karuwar tashin hankali a tsakiyar Mali, wanda yayi sanadiyyar hallaka rayukan mutane 22 a kauyen Koumaga dake yankin Mopti a ranar Asabar.

Guterres ya bukaci a kwantar da hankula, kana ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa dasu kai zuciya nesa tare da lalibo hanyoyin warware rikicin ta hanyar tattaunawar sulhu.

Sanarwar da kakakin ya fitar ta nuna cewa, sakatare janar din ya damu game da samun rahotonnin da suka nuna cewa dakarun tsaron gwamnatin kasar Mali sun aikata laifukan take hakkin dan adam kan al'ummomin yankunan da suka hada da kauyen Nantaka dake yankin Mopti a ranar 13 ga watan Yuni.

Mista Guterres ya bukaci a binciko wadanda keda hannu wajen aikata dukkan laifukan domin gurfanar dasu a gaban shara'a. Game da wannan batu dai, yayi maraba da sanarwar da gwamnatin Mali ta bayar na cewa zata gudanar da bincike tare da daukar matakan ladaftarwa ga wadanda aka samu da hannu wajen aikatan laifukan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China