Rahotanni na cewa, ban da wasu tashoshin jefa kuri'u da aka kai wa hari a arewa da tsakiyar kasar, an gudanar da aikin kada kuri'a cikin zaman lumana a sauran wurare. Jimilar 'yan takara 24 ne suka shiga zaben, amma kafofin watsa labarai na kasar sun ruwaito cewa, zaben ya fi mayar da hankali ne kan manyan 'yan takara biyu, wato shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita da dan takarar jam'iyya mai adawa da gwamnati Soumaïla Cisse.
Za a gabatar da sakamakon farko na zaben ne da safiyar yau Litinin. Bisa jadawalin da kwamitin kula da harkokin zabe mai zaman kansa na kasar ya gabatar, idan babu dan takarar da ya ci rabin kuri'un da aka jefa, za a gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'u. (Maryam)