Sanarwar da majalisar ta fitar a jiyan, ta cewa za a fara bikin sanar da sakamakon ne a da karfe 11 na safiyar ranar Litinin, agogon kasar.
Majalisar ta gayyaci jami'an gwamnati da jakadu da hukumomin kasa da kasa domin halartar taron da za a yi a babban dakin taro na birnin Yaounde.
Da safiyar jiya Juma'a ne majalisar ta kori kara ta karshe cikin 18 da aka shigar gabanta, wadanda ke bukatar soke zaben na ranar 7 ga wata.
'Yan takarar 8 ne suka fafata da shugaban kasar mai ci Paul biya mai shekaru 85, wanda ke neman zarcewa cikin wani sabon wa'adi na shekaru 7. (Fa'iza Msutapha)