in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar kula da kundin tsarin mulkin Kamaru ta yi watsi da kararraki 16 dake bukatar soke zaben shugaban kasar
2018-10-17 10:14:14 cri

Majalisar kula da kundin tsarin mulkin Kamaru, ta kori kararraki 16 daga cikin 18, dake bukatar soke zaben shugaban kasar da aka yi ranar 7 ga watan nan.

Lauyoyin Cabral Libii, dan takarar jam'iyyar adawa ta Univers, sun ce kamata ya yi a soke zaben baki daya, saboda ba a gudanar da shi bisa gaskiya da adalci ba.

Sai dai Mai shari'a Clement Atanga, shugaban majalisar, ya kori karar, yana mai cewa ba a shigar da ita a lokacin da ya dace ba, haka kuma bukatar ba ta da isassun shaidu, sannan ba ta bisa tsarin shari'a.

Har ila yau, majalisar ta kori karar da Maurice Kamto, dan takarar jam'iyyar adawa ta CRM ya shigar, wadda ke tuhumar kwarewa da rashin adalcin mambobi 6 na majalisar.

A cewar Mai shari'a Atanga, shugaban kasar da ya nada mambobin majalisar ne kadai ke da ikon kora ko tuhumar rashin adalcin mambobin majalisar, a don haka, ba za a amince da karar ba.

Bisa tanadin dokar zabe ta kasar, hukuncin da majalisar ta yanke shi ne na karshe, inda kuma ake sa ran za ta bayyana sakamakon zaben a ranar 22 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China