Bisa tanadin dokar zaben kasar, majalisar ce ke da hakkin amincewa da bayyana sakamakon zabe cikin kwanaki 15 da kammala kada kuri'u.
Sanarwar da Sakatare Janar na majalisar, Malego Joseph Asse ya fitar, ta ce a yau Talata ne majalisar za ta fara sauraron korafe-korafe daga wasu 'yan takarar jam'iyyun adawa da kuma masu kada kuri'a dake bukatar a soke zaben.
Daga cikin wadanda suka shigar da kara kotu, akwai 'yan takara masu adawa 3, wadanda ke bukatar a soke wani bangare ko kuma baki dayan zaben, suna masu dogaro da kurakurai da magudi da suka lura an tafka yayin zaben.
Haka zalika, dokar zaben ta yi tanadin cewa, majalisar kula da kundin tsarin mulkin kasar ce za ta yanke hukunci na karshe game da zaben da kuma sakamakonsa. (Fa'iza Mustapha)