A wannan rana, kwamitin ya kori karar da 'dan takarar jam'iyyar adawa ta SDF Joshua Osih ya shigar gaban sa, yana mai bukatar a soke zaben shugaban kasar da aka kada.
Watsi da wannan kara dai ya kawo karshen zaman sauraren korafe korafe da kwamitin ya kwashe kwanaki 4 yana yi, inda ya saurari koke koke 18, wadanda kuma dukkanin su kwamitin ya ce ba su da hujja mai karfi. (Saminu Alhassan)