Paul Nji, ya ce majalisar kula da kundin tsarin mulkin kasar ce kadai ke da ikon bayyana sakamakon zaben, ba wani ba mutum ba.
Wannan na zuwa ne bayan Maurice Kamto, dan takarar jam'iyyar adawa, ya yi ikirarin samun nasara a zaben.
Yayin wani taron manema labarai a birnin Yaounde, Maurice Kamto, ya ce al'ummar Kamaru sun riga sun nuna abun da suke so a bayyana, kuma ya yi niyyar kare Muradin na su har zuwa karshe. A don haka, yake kira ga shugaban kasar mai barin gado, ya shirya mika mulki cikin lumana domin kaucewa duk wani rikicin bayan zabe. Yana mai cewa jam'iyyarsa za ta daukaka zaman lafiya.
Bisa dokokin zaben Kamaru, majalisar kula da kundin tsarin mulkin kasar ce za ta bayyana sakamakon zaben a hukumance, cikin kwanaki 15 bayan kammaluwarsa. (Fa'iza Mustapha)