in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya nuna damuwa game da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Triplolin Libya
2018-09-23 16:05:07 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da majalisar ta jagoranta a Tripoli, babban kasar Libya.

Kakakinsa Stephane Dujarric wanda ya bayyana cikin wata sanarwa, ya ce babban sakataren MDDr ya damu matuka game da yadda ake ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wutar da kungiyoyi masu dauke da makamai suka sanyawa hannu a birnin na Tripoli, karkashin sa-idon mataimakin babban sakataren MDD na musamman mai kula da batun rikicin kasar ta Libya Ghannan Salame.

Jami'in na MDD ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke ba sa ga maicji da juna da su martaba yarjejeniyar kana su guji aikata duk wani abin da zai kara cusa fararen hula cikin akuba.

A jiya da safe ne ma'aikatar lafiyar kasar Libya ta sanar da cewa, fadan da ya barke ranar Jumma'ar da ta gabata a kudancin birnin Tripoli, ya yi sanadiyar rayukan mutane 10 kana wasu 59 sun jikkata, ciki har da fararen hula. Yanzu haka adadin wadanda suka mutu a tashin hankalin kasar ya karu zuwa 106, tun lokacin da fada ya barke a ranar 26 ga watan Agusta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China