in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amfani da sadarwar Intanet a nahiyar Afrika ya ninka har sau 3 cikin shekaru 5, yayin da ake fama da karuwar laifuka a kafar
2018-10-17 10:55:27 cri

Tarayyar Afrika (AU) ta ce nahiyar na daya daga cikin wadanda ke fuskantar karuwar amfani da kafar intanet a duniya, inda amfani da sadarwar intanet ya ninka har sau 3 cikin shekaru 5 da suka gabata.

AU wadda ta shirya taro karon farko, kan laifukan da ake aikatawa ta intanet, daga ranar 16 zuwa 18 ga wata a Addis Ababa na Habasha, ta yi gargadi game da karuwar barazanar dake tattare da ci gaban fasahar sadarwa da hidimomi da manhajoji na zamani.

A cewar AU, yayin da Afrika ta samu ci gaba cikin sauri a fannin amfani da intanet cikin shekaru kalilan da suka gabata, haka gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu, suka fuskanci karuwar barazanar kutsen intanet.

Ana sa ran taron na farko kan laifukan Intanet ya mayar da hankali kan dabaru da dokokin yaki da laifukan, wadanda za su dace da mizanin kasa da kasa da sauran dabarun yaki da irin laifukan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China