in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Jarin Sin a Afirka ya tallafawa nahiyar wajen bunkasa samun 'yanci ta fuskar ci gaba
2018-09-18 19:21:47 cri
Wani rahoto da wasu gungun masanan kasar Sin suka wallafa, ya nuna cewa, jarin da kasar Sin ke zubawa a Afirka, ya yi matukar tallafawa nahiyar, wajen bunkasa samun 'yancinta ta fuskar ci gaba.

Rahoton mai lakabin "Jarin kai tsare da hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka" wanda cibiyar nazarin al'amuran yankunan yammacin Asiya da nahiyar Afirka, da hadin gwiwar sashen nazarin nahiyar Afirka da lura da al'amuran kasa da kasa suka fitar cikin hadin gwiwa, ya nuna yadda jarin da Sin ta zuba a fannin gine gine, ya taimakawa nahiyar a fannin rage tsadar gidaje, da hanyoyin mota, da layin dogo da gadoji.

A hannu guda kuma, hakan na agazawa kasashen nahiyar wajen kyautata kwarewar su ta gudanarwa, da aiki tare da gina manyan ababen more rayuwa, ta hanyar hadin gwiwa a fannin fasahohi da samun horo. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China