in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta musanta yin shisshigin tura dakarun yakar ta'addanci zuwa Mali da Nijer
2018-07-06 10:21:01 cri
Jami'in kasar Algeriya ya musanta zargin tura dakarun soji don yin shisshigi wanda ya wuce ikon kasar a kan iyakokinta da kasashen Mali da Nijer, don yaki da ayyukan ta'addanci.

A wata hira da gidan radiyon kasar, ministan harkokin wajen kasar Algeriya Abdelkader Messahel ya bayyana cewa, Kasarsa bata da hurumin aikata haka, saboda kasar ta tsaya kan matsayinta na gujewa yin shisshigi kan harkokin da suka shafi ikon sauran kasashen duniya.

Yace Algeria ta yi amanna da kiyaye tsaron kan iyakokinta da kuma tabbatar da tsaron kanta ta hanyar yakar ayyukan ta'addanci, ya kara da cewa, ayyukan kare iyakokin kasar aiki ne na kwararru wanda dakarun sojin Algerian suke gudanar da shi.

Messahel yace, rashin yin shisshigin Algeria a harkokin wasu kasashe, hakan ba yana nufin cewa kasar ta killace kanta bane, kuma ba yana nufin cewa ba zata bada gudunmowa wajen yaki da ayyukan ta'addanci bane.

Ya kara da cewa, kasar Algeria tana cigaba da horas da dakarun sojoji masu yaki da ta'addanci a Mali da Nijer da samar musu da kayayyakin aiki da kuma kayan tallafin jinkai ga kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China