in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kula da daidaita yanayi na kasar Sin zai taimakawa Nijeriya wajenn samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba
2018-10-14 16:52:31 cri
A ranar 13 ga wata, kamfanin Elion na kasar Sin ya kulla yarjejeniya da gwamnatin jihar Imo dake kudancin Nijeriya, domin fara aikin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin daidaita matsalar zaman hamada da raya harkokin yawon shakatawa ba tare da gurbata muhalli ba da kuma samar da makamashi mai tsabta da dai sauransu.

A lokacin bikin kulla yarjejeniyar da aka yi a birnin Owerri, babban birnin jihar Imo, shugaban kamfanin Elion Wang Wenbiao ya bayyana cewa, kamfaninsa zai kafa wani babban sansani don daidaita matsalar zaman hamada, da raya harkokin yawon shakatawa tare da kiyaye muhalli da kuma bunkasa makamashi mai tsabta a kasar ta Nijeriya.

Ya kara da cewa, ta hanyar yin hadin gwiwa da Nijeriya, kamfanin Elion zai habaka aikin daidaita zaman hamada na salon Kubuqi zuwa dukkanin yankunan yammacin Afirka, har ma da nahiyar Afirka baki daya. Domin inganta harkokin neman ci gaba ba tare da illa ga muhalli ba, da kuma yin rigakafi da hana yaduwar zaman hamada, ta yadda za a kawar da talauci.

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa, jihar Imo tana da albarkatun iskar gas, ana fatan kamfanin Elion zai bada taimako ga jihar Imo wajen canja albarkatun kasarta zuwa arziki na zahiri, bisa kwarewar kamfanin a fannonin kula da daidaita yanayin kasa, da kuma raya makamashi mai tsabta da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China