Masanan sun yi wannan kiran ne yayin taron kolin nahiyar kan yanayi da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Sun kuma amince cewa, makomar al'ummomin nahiyar na cikin garari duba da yadda dumamar duniya ke haddasa fari da karancin abinci da ma bullar sabbin cututtuka da lalacewar muhallin halittu.
Wani masani dan kasar Habasha kana mutumin da ya jagoranci tawagar MDD mai kula da harkokin gwamnatoci kan sauyin yanayi(IPCC) kan wani rahoto na musamman game da dumamar yanayin duniya Yacob Mulugetta, ya bayyana cewa, karuwar zafi za ta iya mayar da ci gaban da kasashen na Afirka su ka samu a fannonin jin dadin jama'a da tattalin arziki baya.(Ibrahim)