in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasashen Afrika da su rungumi amfani da kayayyaki marasa gurbata muhalli
2018-08-07 11:12:53 cri
Shirin kare muhalli na MDD (UNEP) ya bukaci kasashen Afrika da su rungumi amfani da kayayyaki marasa gurbata muhalli.

Ernest Kamala, jami'ar shirin na UNEP a Afrika, ta fadawa mahalarta taron karawa juna sani da aka shirya a birnin Kampala na kasar Uganda cewa, akwai bukatar gwamnatocin kasashen su dinga sayen kayayyakin da ake sarrafa su daga tsirra domin kiyaye muhalli da kuma samun dauwamammen cigaba.

Ta ce kayayyakin bukacin yau da kullum da ake sayensu su ne kaso mafi yawa na ababen da kasashen duniya masu yawa ke amfani da su.

Kamala ta ce, albarkatun kasa su ne tushen da ake samun duk wasu nau'in kayayyakin da ake amfani da su, da ayyukan hidima da kuma kayayyakin more rayuwa. A cewarta irin yadda al'umma ke amfani da kayayyakin, da yadda ake kula da bada kariya ga albarkatun kasa su ne kadai matakan da za su kiyaye yanayin rayuwar bil adama da kare muhalli da kuma tattalin arzikin kasa.

Ta ce MDD tana tallafawa kasashen duniya wajen bunkasa ayyukan samar da kayayyaki masu tsabta, ta kara da cewa, a shekarar 2015, kimanin dalar Amurka miliyan 11.5 aka ware don gudanar da wasu shirye shirye 34 a kasashen duniya shida, wandada suka hada da Burkina Faso, Ghana, Kenya, Mauritius, Afrika ta kudu da Uganda.(Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China