in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP:Bangaren sufuri na sahun gaba wajen gurbata muhalli a Afirka
2018-09-21 09:52:37 cri

Darektar hukumar kare muhalli ta MDD(UNEP) mai kula da nahiyar Afirka Juliette Biao Koudenoukpo ta ce bangaren sufuri na taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli a nahiyar Afirka.

Jami'ar wadda ta bayyana hakan yayin taron dandalin farfado da harkokin sufuri ta hanyar kirkire-kirkire a nahiyar ta Afirka, ta danganta lamarin da yadda ake shigo da motoci masu shan mai da aka riga aka yi amfani da su, da rashin nagartattun manufofi game da shigo da motoci da karancin abin hannu tsakanin al'ummomin nahiyar.

Don haka ta ce akwai bukatar kasashen na Afirka su tsara matakai da manufofi game da ma'aunin ingancin iskar shaka, duba da yadda bangaren sufurin nahiyar ya kasance a sahun gaba wajen fitar da gurbatacciyar iska da sauran abubuwan masu gurbata muhalli, wadanda ke yin mummunan tasiri kan muhalli da ma lafiyar al'umma.

Amma kuma wasu daga kasashen nahiyar, kamar Cote d'Ivoire sun bullo da matakan kula da ingancin iskar shaka, baya ga matakan sanya ido da suke kokarin dauka.

Shugaban sashen kula da ingancin iska da ababan hawa na hukumar kare muhalli ta MDD Rob De Jong, ya kalubalanci gwamnatocin kasashen Afirka, da su fito da shirye-shirye game da amfani da motocin haya da ababan hawa masu amfani da wutar lantarki da ma ababan hawa masu sarrafa kansu.

Ya ce, UNEP tana taimakawa kasashen Rwanda da Kenya da Najeriya, kan yadda za su samar da hanyoyin gefen titi da jama'a za su rika amfani da su a cikin biranen kasashen.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China