Bugu da kari, ministocin sun amince su kara inganta kwarewar ma'aikata ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa a Afirka da zuba jari a fannonin kirkire-kirkire don canja hanyar samun bunkasuwa ta yadda za a kai ga samun ci gaba mai dorewa, maimakon matakan da ake amfani da su a halin yanzu da ba sa samar da sakamako mai kyau cikin hanzari.
Ministocin sun kuma amince su goyi bayan tsare-tsare game da muhalli na kasashen Afirka don yayata da musayar kwarewa da mafita a sassa daban-daban na nahiyar. Za kuma su kara karfin kasashensu wajen aiwatar da manufofi da dokoki da shirye-shirye don karfafa matakai da sauran shirye-shiryen kula da muhalli.
Daga karshe ministocin sun yi kira ga babban taron MDD kan muhalli da shirin kare muhalli na MDD da su kara goyon bayan da suke baiwa kasashen Afirka da ma saukaka musu hanyoyin yin hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire.(Ibrahim)