in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta fara aiwatar da shirin dakile gurbatar iska
2018-07-04 09:55:24 cri

Mahukunta a Najeriya sun lashi takobin aiwatar da wasu sabbin matakai na dakile gurbatar iska, a matsayin wani mataki na inganta kiwon lafiyar al'ummar kasar.

Da yaka bayyana hakan, yayin wani taron fadakar da jama'a a jihar Gombe dake arewa maso gabashin kasar, darakta a hukumar dake lura da nagartar muhalli ko NESREA a takaice Mr. Wuave Daniel, ya ce hukumar ta fara hadin gwiwa da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, wajen aiwatar da sabbin dabarun dakile gurbatar iska.

Ya ce, shirin wanda ya shafin lura da hayakin da ababen hawa da injunan samar da wutar lantarki ke fitarwa, na da nufin rage irin wannan nau'in hayaki domin kare lafiyar jama'a.

Mr. Daniel ya ce, za a rika samar da cibiyoyin auna ingancin iska a sassa daban daban, inda za a rika tantance nagartar iskar, domin tabbatar da ta dace da bukatun lafiya na al'umma.

A daya hannun jami'in ya ce, za a wayar da kan masu amfani da injunan samar da wutar lantarki, game da dokokin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, ko mai cutar da lafiyar jama'a, ciki hadda yawan yiwa irin wadannan injuna sabis domin rage yawan hayakin da suke fitarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China