Trump ya fadawa 'yan jaridu a White House cewa, Powell, tsohuwar babbar mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro, ita ce wacce ake magana a kanta, a lokacin da aka tambaye shi ko ita ce take sahun gaba cikin jerin mutanen da ake sa ran za su gaji Haley, wacce ta sanar da yin murabus dinta a ranar Talata.
A ranar Talata ne, Trump ya bayyana cewa ya riga ya tanadi sunayen mutane 5 wadanda ake sa ran daga cikinsu za'a nada wannan mukami. Ana sa ran shugaban zai bayyana sunan sabon jakadan Amurka a MDDr cikin makonni biyu ko uku masu zuwa.
Trump ya amince da yin murabus din Haley a ranar Talata, sai dai za ta cigaba da zama kan wannan mukami har zuwa karshen shekarar nan da muke ciki.
Powell ta koma Goldman Sachs da aiki a matsayin babbar jami'a bayan da ta bar aiki da fadar White House a farkon wannan shekara. Ta taba yin aiki da gwamnatin George W. Bush. (Ahmad Fagam)