in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump zai gana da shugaba Kim bayan zaben rabin zango
2018-10-10 14:36:02 cri
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka, zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa bayan kammala zabukan tsakiyar zangon mulkin shugaban na Amurka, zaben dake tafe a farkon watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaba Trump ya bayyanawa 'yan jarida hakan a kan hanyar sa ta zuwa jihar Iowa, inda ya ce yanzu haka ayyukan yakin neman zabe sun masa yawa, ta yadda ba zai iya shirya ganawa da shugaba Kim ba.

Shi ma a nasa bangaren, yayin wata zantawa da manema labarai a fadar White House da yammacin jiya Talata, ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya jaddada nasarar da Amurkan ke samu, game da burin ta na raba zirin Koriya da makaman kare dangi.

A ranar 12 ga watan Yunin da ya gabata ne dai shugabannin kasashen biyu suka yi ganawar farko a Singapore. Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanyawa hannu, shugabannin biyu sun amince Amurka ta samarwa Koriya ta Arewa kyakkyawan tsaro, yayin da ita kuma Koriyar za ta aiwatar da matakan raba zirin Koriya da makaman kare dangi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China